𝐒𝐇𝐀𝐖𝐀𝐑𝐀
Yawan tsawaita lokaci wurin neman aure shike sabbaba mafi yawan matsalolin da muke fuskanta kafin auren wasu ma har bayan auren.
Haɗuwar da za'ayi cikin wata ɗaya ko makamancin haka ayi auren a lokacin tafi sauqi da sauqaqama kowanne bangare wurin ɗawainiya da rufe qofar duk wasu matsalolin da muke fuskanta.
Matakin kawai shine kai namiji idan kasan baka shirya aure ba tun farko to ba ruwanka da shiga sabgar ɗiyar mutane, sam babu wata alaƙa da zaka ƙulla da ita, ka bari sai lokacin da ubangiji ya baka damar abunda za ka iya riƙe iyalin dashi ka shirya tsaf, sai kaje ga batun neman auren
Kema 'yar uwata ki kame kanki da mutuncinki ki tantance mijin aure da mijin ɓata lokaci, ki tabbatar duk abinda zakiyi da sanin iyayenki akai, ki sani mace tafi shan wuya a matsalar soyayya musamman irinta yanzu, kuma lokacinki ba kamar nasa bane, kar kibi son zuciya kizo kina dana sani.
Soyayya ta gaskiya sai bayan aure take tabbata kuma itace wacce ake buqata ba irin wannan ta ɓata lokaci da bin son rai ba, addini akace mu zaɓa da tarbiyya ta gari idan har an samu waɗannan to cikinsu za'a sami dukkan abinda ake nema.
Haɗuwa ɗaya ko biyu ta isar da a sami fahimtar juna waliyyai suyi ƙwaƙƙwaran bincikensu daga nan aure ya tabbata, sai kaga kowanne bangare basu taƙura ba, anyi abun cikin sauƙi da tsari na shari'a, shikenan an wuce wurin.
Sai mun gyara mun cire son zuciya mun bi koyarwar shari'a sannan Allah zai gyara mana.
Allah ya sa mu dace.
