Gaskiya tana da nauyin ɗauka, ba za ka gane hakan ba sai lokacin da ka yi kuskure, ko kake kan kuskure, aka ba ka gyara. A nan za ka ji zuciyarka na kumbura, kanka na ɗaukar zafi saboda an kawo abin da ya saɓa da naka tunanin.
Wasu na cewa gaskiya na da ɗaci, ai dole ta yi ɗaci. Gaskiya magani ce ga cutar ƙaryar; ka sassauta faɗar ta cikin sanyi, da usulubi mai kyau, ba da niyyar fariya, tozartawa ko tunzurawa ba, mai rabon shiriya zai karɓa. Faɗa ce taka, amma shiriya ta Allah ce.
Kana yi wa wani kallon ɓata, ya dulmiya cikin shirka da bautar mutane, shi ma yana ma kallon ɓatacce, maƙiyin waliyan Allah. Wasu ba su gane bambanci Larabci da nassi, komai idan aka faɗa da Larabci hujja ne a wurinsu.
A Musulunci, TAUHIDI shi ne farko!
Bayan Allah, ba wani abun bauta, 'لا شريك له';
Duk wanda ya ce ka bautawa wanin Allah, ya zalunce ka, ya ɓatar da kai. Ba a yi wa kowa bauta da gaɓɓai ko ruhi sai Allah (shi kaɗai). Ba a neman taimakon kowa, 'isti'ana', 'istigatha' da 'isti'adha' sai a wajen Allah. Kama sunan wani mutum da sunan neman biyan buƙata shirka ne, a cikin annabawa, mala'iku, waliyyai ko shehunnai.
Ba a wani mahaluƙi mai girma da daraja cikin bayin da ya kai Manzon Allah ﷺ. Abin da ya zo da shi, shi ne Shari'a, shi ne shiriya. Ba wani da zai zo da wani sabon abu da kai nasa daraja. Duk ijma'i da ƙiyasi da malamai za su yi, fahimta ce mai naso daga nassi, ba (wai) kawo sabon abu ba.
Duk wanda ya faɗa ma gaskiya, ba maƙiyinka ba ne, MASOYI ne da yake son fitar da kai daga halaka da ɓata na shirka. Addini ba (iya) yadda ka taso ka ga ana yi a gidanku ne kawai gaskiya ba, gaskiya tana cikin nassosi. Ba iya abin da malaminka kaɗai yake faɗa ma ne gaskiya ba, ka buɗe zuciyarka, ka yi karatu, ka nemi shiriya a wajen Allah.