Hujjar Mu Ta Goyon bayan Abinda ya Faru A Gabon

Hujjar mu ta goyon bayan abin da ya faru a Gabon.

(1)  Muna son mulkin soja a Nijeriya saboda demokraɗiyyar ta kasa tsare rayukan mu da dukiyoyin mu. 
A yau ta'addanci ya zama ruwan dare birni da ƙauye(commonplace), a yayin da masu mulkin mu na demokradiyya suka yiwa rayuwar mu riƙon sakainar kashi (soft-pedaling).

(2) Masu mulkin mu sun maishe da demokradiyyar faggen kasuwancin su, sun ja malaman mu na addini ( Yes clerics) a jikin su, dan suji daɗin zaluntar mu. 
Sun yunwata mu (starvation), dan su sami ikon juya mu ta yanda suke so. Hakan tasa muke sayar da 'yancin mu ( kuri'a ) a ɗan kuɗi kadan, saboda kangin talauci ya rufe mana idanu (object poverty) ba'a ta walwalar mu (social welfare).

(3) A yau duk masifar rashin tsaro da wannan demokradiyyar ta haifar, yaran sojojin mu ne ke girbar ta fiye da kowa, domin su suka tari masifar (at war front) har takai ga asarar rayukan su, a inda kuma masu mulki demokradiyyar suna can suna barci cikin aminci ( with air condition) da iyalen su.

(3) Bama buƙatar tsarin domin ya kasa samar mana da ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.

Amsar mu ga masu cewa mulkin soja zai hana ka faɗin albarkacin bakin ka (freedom of expression) da kuma tursasawar rayuwa (coercion)  : 

Shin yanzu da demokradiyyar ta baku 'yancin faɗin albarkacin bakin naku me surutun naku ya samar mana? 
Ya dakatar da zaluncin da ake mana 🙄  eye ?
ko kuma ku dai surutun ne muradin ku a rayuwa? 
Tursasawa akan ayi daidai abu ne me kyau (disciplinkishine) kenan. Domin sangarcewa ce sillar matsalar da muke ciki.
Dan haka mu fatan Allah ya sa wani sojan ɗan  ƙasa ya karɓe mulkin daga hannun wannan azzaluman tsofaffin dan mu sami mafita daga rashin tsaron dake addabar mu.

#Salim_A_Lere
Previous Post Next Post

Contact Form