Kafin ka yanke hukuncin labari daga ɓangare ɗaya,
Kafin ka fara tsinewa ɓangare ɗaya...
Yana daga cikin alamar cikar hankali, idan mutane 2 da ka sani suna ƙaunar juna, yaro ko ubangida, abokai, masoya ko ma'aurata, ɗayansu ya kawo ma gulmar rashin kirkin ɗaya, bayan ka gama ji, ka ce: "NA JI DAGA BAKINKA, SAURA DAGA BAKINSA"
Sau da yawa, mai bada labari na bada labarin yadda zai wanke kansa ne, ya ɓata abokinsa ne, kai kuma cikar hankalinka zai sa ka yanke hukunci bisa adalci.
Misali:
1. Mahaifiya ce ta samun Ubangidan ɗanta don kwata wa ɗanta haƙƙi ƙin biyan kuɗin aikin da yake masa. Maigida ya ce, bai taɓa danne masa haƙƙi ba, hasali ma, shi yake bin sa bashin wasu kuɗaɗe da ya karɓi bashi, kuma ya ha'inci wasu customers da suke harkokin kasuwanci da su. Yaron ya haɗa maganar ne don kar yana taimakawa mahaifiyar da 'yan kuɗaɗen da yake samu. Zagi da tsinuwa nawa maigidan nan ya sha a wajen mahaifiyar yaro, da 'yan gidan su yaro?
2. Mata ta kai ƙarar miji wajen iyayenta, kan ya zafafa wajen sanya mata ido, kuma yana yawan yi mata fushi. Mahaifin da ya ƙira mijin, sai miji ya buɗe sirrin da ya rufa mata na cewa, idan ta dawo gida daga aiki, tana ci gaba mu'amala da abokanta maza na wajen aiki da wasu mazan a social media, ba ta ba shi lokaci, tana mantawa da haƙƙin aure dake kanta.
3. Aboki ne kullum ya zauna a majalissa yana labarta amininsa ba shi kirki. Da aka bibiyi magana, sai aka samu bashin kuɗinsa ya karɓa da yawa ya ƙi biya, da aminin nasa ya nuna yana buƙatar haƙƙinsa saboda an ɗauki tsawon lokaci, sai mai taimako ya koma maras kirki.
✍️Aliyu M. Ahmad
22nd Shawwal, 1444AH
12th May, 2023CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
Photo Credit: LSD Daily
